LABARIN WANI SAURAYIN DA YAKE TURA SAKO NA EMAIL ‘DIN BATSA DAGA KABARIN SA

0
90

Wani mutum yake ba Dr. Muhammad Abdurrahman Al-arefe na kasar Saudiyya labarin wannan abin da ya faru. Mutumin yana cewa:
Ina da wani aboki ya mutu, sai wani abu ya biyo bayan mutuwar sa, ina fatan Allah ya jikan sa, kuma ya rinjayar da ayyukan sa na Alkhairi akan ayyukan sa na sharri, ba wai mutuwar tasa bace babbar matsalar da ta dame ni ba, domin ko wannen mu zai mutu, sai dai babban damuwan da ke cikin mutuwar ta sa itace:
“Yana da wani mugun aiki dake gudana ta email dinsa, wanda tun
yana da rai ya kasance yana son
website dinda suke yada hotunan
batsa. Har ma sai da yayi tarayya
da wani website na ‘batanci, ya
biya su kudi sunatura masa da batsa lokaci bayan lokaci. Har ta
kai ga ya’kara biyan wani kudin
tare da bada email din abokan sa
don a dinga tura masu da hotunan batsan da sunan shi,da kuma kudin sa, a duk sanda wannan website din suka samu wani sabon batsa.
Kwasam! sai ya mutu, kuma
babban abin damuwa shine ba wanda ya san number sirrinsa na wannan website ko email din domin mu tsayar da wannan sakon da ake aikawa mutane da sunan sa, na tsaya ina ta tunanin yanda za’ayi, alhalin kuma ina cikin masallaci ina jiran ayi masa sallar gawa, bayan an yi masa sallah aka dauke shi a kafada muna tafiya zuwa makabarta, sai wani tunani ya fado min yanzu me wannan bawan Allah zai gani a kabarinsa… Hotunan batsa?

Hasbunallahu wa ni’imal wakeel.
Bayan mun kai makabarta, na duba kabarin da za’a birne shi, na sake duba cikin kabarin Hmm!
Yanzu ya yanayin sa zai kasance a cikin wannan kabarin? A kewaye da kabarin kuma ga mutane suna ta kuka, bayan mun birne shi muka barshi a cikin duhun kabari shi kadai, sai mu da ‘yan uwansa da dukiyarsa muka juya zuwa gida, ba abinda ya sauran masa face aikin sa.
Bayan haka sai mahaifiyarsa ta yi mafarkin yara suna zuwa yin fitsari akan kabarinsa, abin ya daure mata kai, sai take bamu labarin abin da ta gani a mafarkin kuma tana son ta san meye ma’anar wannan mafarkin, ita kuma uwar bata san labarin abin da yayi kafin mutuwarsa ba, sai na fadi a zuciyata: Ai wannan mafarkin baya bukatar neman fassara domin ma’anar sa a bayyane take, wainnan yaran da ta gani a mafarki suna zuwa yin fitsaria kabarin nasa, sune
mutanen nan da suke tura masa hotunan batsa da shi da abokanen sa, Ya Salam! Yanzu ya zai iya daukan nauyin wainnan laifukan? Ya zayyi da nauyin nasa ballantana har da na abokanen sa?
Nayi Kokarin na kyautata masa, sai na kira website dinda suke turo masa da abokansa wainnan
abubuwa na batsa, don su tsayar
da turo masa da wainnan sakunan,su kuma cire shi cikin wannan tsarin, sai dai basu yardaba, kuma suka nemi uzuri a wajena, suka ce ai duk wanda ya
shiga tsarin yana da number
sirrinsa don haka na basu number, Na ce masu Shi mutumin ya mutu!!! Ko kulani basu yi ba.
Na zauna ina ta tunanin wane irin
hali yake ciki yanzu! Sai na tuna
da Hadisinda Manzon Allah (SAW) yake cewa: “Lallai daga cikin mutane akwai masu rufe alkhairi
kuma su bude sharri”.
Kai! ina tunanin shima wannan bawan Allah yana cikin su, sau
nawa nake ta yi masa fada, amma
yaki dauka. Ina ce masa: “Shin zaka iya daukar nauyin zunuban mutane? Ya zaka zama mabudin sharri? Ya zaka dauki nauyin laifin da suka aikata a wuyanka ranar Alqiyama? Sai dai a wannan lokacin yaki karban nasiha ta, yana ganin ai shi matashi ne, kuma ma wannan ai don ‘debe kewa ne, Subhanallahi!mu tane nawa ne cikin matasa suka kalli wani hotonbatsa kuma suka abkawa alfahsha sanadiyyar
haka?
Labarin sa ta kare”. Da wannan ne ni kuma nake cewa muji tsoron Allah, mu gyara ayyukan mu, kuma dukwani page din da muka yi liking muka san cewa na batsa ne ko kuma suna sa hotunan batsa wani lokaci damu fita daga wannan page din, saboda bamu san sanda zamu mutu ba, kuma mun san ba wanda muka sanar dashi password din mu, kamar dai yanda muka ji ya faru ga wannan bawan Allah din. Kullum Malamai kokarin farkar da mutane suke yi musamman a Facebook da whatsapp amma mutane suna daukan sa wasa sun manta abin da Allah yake cewa:
( ﺇِﻧَّﺎ ﻧَﺤْﻦُ ﻧُﺤْﻴِﻲ ﺍﻟْﻤَﻮْﺗَﻰٰ ﻭَﻧَﻜْﺘُﺐُ ﻣَﺎ ﻗَﺪَّﻣُﻮﺍ
ﻭَﺁﺛَﺎﺭَﻫُﻢْ ۚ ﻭَﻛُﻞَّ ﺷَﻲْﺀٍ ﺃَﺣْﺼَﻴْﻨَﺎﻩُ ﻓِﻲ ﺇِﻣَﺎﻡٍ
ﻣُّﺒِﻴﻦٍ )
((Lalle Mũ, Mũ ne ke rãyar da
matattu kuma Mu rubũta abin da
suka gabãtar, da gurãbunsu,
kuma kõwane abuMun ƙididdige
shi, a cikin babban Littãfi
Mabayyani)
(ﻳَﻮْﻡَ ﻳَﺒْﻌَﺜُﻬُﻢُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺟَﻤِﻴﻌًﺎ ﻓَﻴُﻨَﺒِّﺌُﻬُﻢ ﺑِﻤَﺎ ﻋَﻤِﻠُﻮﺍ ۚ
ﺃَﺣْﺼَﺎﻩُ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﻧَﺴُﻮﻩُ ۚ ﻭَﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻰٰ ﻛُﻞِّ ﺷَﻲْﺀٍ
ﺷَﻬِﻴﺪٌ )