Cikakken Tarihin Sheik Jafar Mahmud Adam

0
42

Haihuwa Da Fara Neman ilmin Mallam Ja’afar Mahmoud Adam

An haifi marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam ne a garin Daura, a farkon shekarun 1960s.

Marigayi Ja’afar ya fara karatunsa na allo a gidansu a Daura, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini.

Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari “Koza” da ke Arewa da Daura a jihar Katsina. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami a 1971 sai ya zauna a makarantar Malam Abdullahi a cikin Fagge.

Dama can Sheikh Ja’afar ya riga ya fara haddar Alkur’ani maigirma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malamin ya haddace Alkur’ani ne sai ya ga bukatar ya samu ilmin Boko don haka ya fara karatun zamani a 1980.

Har wa yau, Malam Ja’afar ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al’adun kasar Misra (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar Boko ta manya watau “Adult Evening Classes.”

A 1983 ne Malamin ya kammala wadannan makarantu 2 na Boko da Arabiya, wanda daga nan ya samu shiga shiga makarantar GATC Gwale a 1984, har ya kammala a1988. Bayan shekara guda ne ya wuce Jami’ar Musulunci ta Madina.

A wannan babbar jami’ar musulunci ta Madinah ne Malamin ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur’an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. A wancan lokaci ne aka soma jin tafsirin sa na Al-Qur’ani a cikin Garin Maiduguri.

Bayan nan Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci ta Oundurman a kasar Sudan.

Kafin rasuwar Malamin, yayi nisa wajen karatunsa na PhD) a Jami’ar Usman Danfodio ta Sokoto.