HALASTA LUWADI KO MADIGO BA RA’AYIN AMINA BANE KADAI

0
23

Daga Abu Ahmad

Kusan daga jiya lahadi labarin dayafi yawo a kafofin yad’a labaru musamman na najeriya shine batun da akace wakikiya a majalisar dinkin duniya wacce akace sunanta Amina Muhammed ta amince tare da sanya hannu kan dokar auren jinsi. Ma’ana a wannan batu shine, an yarda mace ta auri yar uwarta mace (Madigo) su kuwa maza zasuyi nasu auren don aikata (Luwadi).

Ganin wannan labari naji ra’ayin wasu mukulisan bayi inda suke nuna rashin amincewa da kuma Allah wadai kan wannan mataki, sede sun manta wani al’amari guda daya.

Ita wannan mata (Amina) ma’aikaciya a majalisar MDD Itace mataimakiyar babban sakataren majalisar tana wakiltar najeriya ne a wannan zaure, don haka duk wani qudiri ko Doka wacce za’a kawo din neman amincewar wakilai, dole Amina ta nemi amincewar ko shawarar gwamnatin najeriya kark’ashin Buhari kafin ta furta wani abu akwai. Kunga kuwa ashe ba Amina bace ta amince da wannan mummunan al’amari face yan najeriya (Ammafa banda ni).

Wani abin takaici shine, ita wannan doka ba tun yanzu ake neman najeriya ta amince da itaba, lokacin tsohon shugaba Good L. Jonathan an nemi anyi, amma yaqi amincewa bisa dalilin shi na cewa, dukkan wad’annan dabi’u da ake neman a amince dasu sun sabawa addinai da al’adun yan najeriya.

Kuma koma menene, a matsayinta na musulma babu dalili na kusa ko na nesa da har zata amince da bukatar Buhari cikin wannan iskanci.
Don haka kada ku zargi Amina da aikata komai amma Ku zargi kan Ku ta hanyar kawo daqiqin shugaba.

Ya Allah kada ka kamamu da lefin wawayen cikinmu.