Kiristoci ne suka taimake ni lokacin da Musulmi suka juya min baya – Buhari

0
71
buhari
NIGERIA PMB

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna bacin ransa a kan halayen wasu ‘yan Najeriya da ke amfani da kabilanci ko addini domin aikata zalunci da aikata rashawa inda ya ce yaudara ce da shirme.

A jawabin da ya yi a wurin taron cin abinci na musamman inda ya gayyaci tsaffin abokan aikinsa yayin da ya ke mulkin soja (tsakanin 1984-1985) da aka gudanar a ranar Lahadi a fadar Aso Rock, shugaban kasar ya ce rashawa ce ke sanya wasu boyewa cikin rigar addini da kabilanci.

Domin kafa hujja a kan abinda ya fadi, shugaban kasar ya bayar da labarin gwagwarmayar da sha a kotun zabe a shekarun 2003, 2007 da 2011 inda ‘yan uwansa musulmi ‘yan arewa ne suka kayar da shi yayin da Kiristoci daga kudu ke kare shi.

“Wasu dalilai sun sanya ni magana a kan wani da nake matukar mutuntawa a Najeriya. A 2003 da na fara, ana fara shigar da karar zaben shugaban kasa ne daga kotun daukaka kara. A lokacin shugaban kotun ajin mu daya da shi a makarantar sakandire, ni da shi da Shehu Musa Yaradua duk ajin mu daya. Lauya na a wannan lokacin, Mike Ahamba kirista ne kuma Ibo. Zuwa na kotu ranar farko, Ahamba ya ce min yana bukatar jerin sunayen wadanda su kayi rajistan zabe a wasu yankuna domin ya nuna cewa kuri’un da aka samu a wuraren na bogi ne. Ya bukaci su rubuta bukatarsa kuma su rattaba hannu, kuma su kayi hakan.

“A yayin da suka zo yanke hukunci, sai suka ki ambaton zancen. A cikin jerin alkalan wani Kirista kuma dan kabilar Ibo ne ya daga hannunsa ya tunatar da su abinda lauya na nema. Shin mun nemi a bamu rajistan wadanda su kayi zabe a wadannan yankunan? Idan ba muyi ba kuma menene dalili? Nan suka yi masa taron dangi suka ce ya yi shiri. Hakan yasa ya rubuta hukuncinsa daban da nasu. A yau shine jakadar Najeriya a Amurka.

“Na shigar da kara a kotun koli. Wanene babban alkalin kotun? Musulmi ne Fulani daga Zaria. Bayan watanni 27, mun sake komawa kotun. Ahamba ya yi bayani na sa’o’i 2 da mintuna 45 amma suka ce masa za su tafi hutu a goben ranar. Sunyi hutu na watanni 3 kuma da suka dawo hutun su kayi watsi da shar’ar namu cikin mintuna 45.

Source: Legit