Ya kai iyayensa kara saboda sun haifeshi ba tare da neman shawararshi ba

0
63

Wani mutum dake garin Mumbai a India ya yanke shawarar zai kai iyayensa kara saboda sun haifeshi ba tare da neman shawararshi ba. Wanda yace haka ya sabawa tunaninsa. Mutumin wanda ya yace shi bai tsani iyayensa ba ko kadan amman haifarshi ba tare da izininsa ba wannan babban kuskure ne.

Ina son iyayena sosai. Muna da dangantaka sosai tsakanina dasu kuma sun haifeni ne saboda fatin cikinsu da jin dadinsu.

Mutumin da. Shekara 27 wanda ya rufe fuskarshi da gilashi sannan kuma da gemun karya a shafinsa na Facebook. Yayi wannan ikirarin ne a shafin nasa na Facebook imda yace duk da haka kuma yana son iyayensa sosai.