An kama mutane 140 da suka shirya yi ma Buharu juyin mulki

0
96

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Enugu a karkashin jagorancin Alkali mai sharia A.N Chioke ta bada umarnin garkame wasu tsagerun yayn kungiyar rajin kafa kasar Biyafara ta IPOB bisa tuhumar da Yansanda suke musu na shirya yi ma shugaban kasa Buhari juyin mulki.

An ruwaito a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu ne Yansanda suka taso keyar tsagerun a cikin motocin bas bas kirar 608 da kuma wata mai cin mutane 18 zuwa kotun, inda ake tuhumarsu da aikata laifin cin amanar kasa.

Sai dai saboda tsananin yawansu hakan yasa a farfajiyar kotun aka gudanar da zaman shari’ar tasu domin kuwa dakin kotun ba zai daukesu ba, Dansanda mai shigar da kara ya bayyana cewa laifin da tsagerun suka aikata ya saba ma sashi na 516 (A) na kundin dokokin Najeriya.