Ganduje yaso ya tsige Sarkin Kano

0
54

Wata majiyar gwamnatin Kano ta bayyana yadda gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya so ya tsige sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ba don Alhaji Aliko Dangote ya gaggauta shiga tsakani ba.

An zargi Sarki sunusi da wawure wasu kudade a masarautar Sarkin kanon.

A majiyar tamu ta shaida mana cewa “Amma sai Ganduje ya shaida wa Dangote cewar ya koma ya sanar da Sanusi II cewar yana da zabi guda uku; ko ya yi murabus da kan sa ko gwmnati ta tsige shi ko kuma ta kirkiri karin sabbin masarautu hudu a jihar.