Daga Farfesa Ibrahim Malumfashi Zuwa Ga Shugaba Muhammadu Buhari (3)

0
24

Zuwa Ga Shugaba Muhammadu Buhari (3)

Shin da gaske ne cewa kana ta kokarin motsawa, amma wasu ne da ba sa son mulkinka suka hana maka sakat, shi ya sa abubuwa uku da gwamnatinka ta yi niyyar aiwatarwa don ci gaban kasa; wato tabbatar da tsaro da tayar da komadar tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da almundahana suka gagara kawar wa ko samar wa?

Shin hujjojin da masu bibiyar mulkinka, musamman masu mutuwar son ka da tsarin mulkinka suke bayarwa na cewa laifin ba naka ba ne, na wasu ne, shin hakan gaskiya kuwa? Ina tabbatar maka ba gaskiya ba ne, bisa dukkan alkalumman adalci da za a yi amfani da su.

Ba kamar sauran masu nazarin tsarin mulkinka da kuma yadda kake gudanar da shi ba, ni ina da yakinin tabbas ka gaji kasa da gwamnati da tattalin arzikinta suka durkushewa ta kowace irin fuska mutum ya duba, musamman abin da ya shafi tattalin arzikin kasa da ya kasance cikin masassara dab da hawanka mulkin kasar nan, ka kuma yi iya kokari wajen ba shi kuni da ya sha ya fara farfadowa, amma ka sani, kamar yadda sauran al’umma ta sani, jinyar tattalin arzikin kasar nan yanzu ma aka fara, ba kuma wani abu ya hana a yi wa tattalin arzikin tiyata ba, sai rashin wani dabashiri domin fuskantar wannan kalubale.

Ba kuma wani abu ya jawo haka ba daga cikin wasu daliliai da ya wuce na rashin wani dawwamammen tsarin gina kasa ta fuskar tattalin arzikin da ya dace, ba wai duba da bitar shifta daga littafin abin da Bankin Duniya ko Hukumar Lamuni ta Duniya suka bude maka ba. Ba tun yau ake fada ba, wadannan hukumomi, ba ‘yan gatan kasashe irin Nijeriya ne ba, ‘yan gatan jari-hujja ne, ba talakawa da ke cikin kunci da damuwa ba a kasashen da ke tasowa a duniya.

Na san za ka ce da ni ai an yi kokarin fitar da A’i daga sana’arta ta rogo a fagen tsarin tattalin arzikin kasar nan, ni kuwa sai na ce da kai, uwar kudin ma ba a fitar ba, balle kuma uwa-uba riba, har yau A’i, wato talakawan Nijeriya ba su ji ko gani ba, in kuwa sun ji da gani, to ba dai sauki ba, sai dai kunci da damuwa!

Ya Shugabana, ba ina ganin wallenka ba ne a nan, matsalar ita ce, dukkan inda ka ji ana ta cewa sa toka sa, sa katsi, musamman a fagen gyaran tattalin arzikin kasa, to baba ne ya yi gardama. Matsalar tattalin arzikin kasar nan da yake some a halin yanzu a matakan ruhi ne da aiwatarwa in ana son a ga an kai ga gaci, ba matakan zama a ofis domin shan iska da dogon turanci ba da muke gani a halin yanzu.

Ga misali, gwamnatinka a cikin shekarun da ta yi tana mulki ta mayar da hankali ne wajen gine-gine da sassake-sassake da buge-buge da rushe-rushe, domin samar da hanyoyi ko dogo da taragon jiragen kasa ko kwaskwarimar masana’antu da wasu kamfanoni da nome-nome don samar da amfanin gona da kayayyakin sarrafawa a kamfanoni da abincin ci, yin haka a tunanin gwamnatinka zai inganta farashin kayayyakin da ake sarrafawa da samarwa da kuma samun kudaden shiga a cikin kasa, domin a ci dunun dokin cigaba, a kuma inganta komadar tattallin arziki ta fuskar (Madubin Tattalallen Cigaban Kasa), GDP.

Ni dai ba masanin tattalin arzikin kasa ba ne, to amma abin da ke tashe yanzu a duniyar inganta tattalin arziki a duniya kamar yadda masana harkar ke bayani, shi ne a ‘tayar da komadar tattalin arzikin talakawa da sauran al’ummar kasa,’ ba wai tayar da komadar tattalin arzikin kamfanoni da ‘yan jari-hujja ba,’ wanda shi ne gwamnatinka ta sa gaba.

Ka sani ya Shugaba Muhammadu Buhari, masana tattalin arzikin kasa tuni sun gano cewa kasashe irin Nijeriya ba za su taba fita daga tarkon masassarar tattalin arziki ba, har sai sun tayar da komadar tattalin arzikin talaka da marasa karfi, ba kuma wata hanya da ta dace a bi da ya wuce a sa kasafin kudin kasa ya fuskanci al’ummurran da suka shafi talaka kai tsaye, kamar samar da ingantaccen ilimi ga yawancin al’ummar kasa da rage radadin talauci ga yawancin talakawa da yara kanana, ba wai tsarin trader moni ko n-power ko wani adashin gatar da bai fitar da mutane daga damuwa da kunci ba.

Wata hanyar gyara kuma ita ce a samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga yawancin al’ummar kasa, shi ma mataki ne na auna ci gaba, ba wai makalewa tattalin GDP kawai ba, da a takarda yake kwana da tashi, sai kuwa a asusan ‘yan jari-hujja. Ke nan tsarin tattalin arzikin da muke gudanarwa a halin yanzu ya Shugaban kasa, ya yi ban-hannun-makafi ne da abin da ke tabbatacce da halin rayuwar talaka. Ka ga ke nan, i jiya, i yau, kila ma i gobe ko har abada, in ba gyaran kwarai aka yi ba. Allah ya kyauta!

Saboda haka ya Shugabana, lokaci ya yi da za ka samar da dawwamammen tsarin tattalin arzikin da zai sa talakawa farin ciki da annashuwa, kada su kasance sun yi zaben-tumun-dare, sai safiya ta yi su rasa abin sa wa a bakin salati. Ka dai san irin halin kuncin da al’ummarka ke ciki, ka fada, ba sau daya ba biyu ba, amma kullum na yi nazarin tsarin da kake bi na gudanar da tattalin arzikin kasar sai na ga tamkar madubin da kake amfani da shi, na duba-rudu ne, ko mai zagi, domin ni abin da nake hangowa kai ba shi kake hangowa ba, ban sani ba, ko kai ba ka ji a jikinka ne, kamar yadda mu muke ji! Ga hujja!

Za Mu Ci Gaba