Makarantar Islamiya zan koma bayan na sauka daga kan Mulki ____Gwamnan Adamawa Bindow

0
103

Gwamnan Adamawa Muhammad Ummaru Jibrila Bindow yace makarantar islamiya zai koma saboda ya kara samun ilimin qur’ani bayan ya sauka daga kan mulki ran 29 ga watan Mayu.

Gwamnan ya fadi hakan ne a wani shirin gidan radion adamawa Taba kidi taba karatu inda yace “ina son zuwa sudan akwai makarantun islamiya a can, ina son kara karatu”

“Ina son naje Sudan don na ‘kara karatun addinina a can” inji Bindow.

Ya kara da cewa “Akwai maigidana a can Alhaji Adamu da sauransu ina son naje na gaishesu. Ko na bar Abuja a 29 ga watan mayu ko kuma ban bari ba amman dai burina shine naje Sudan din na karo ilimi”

“Sannan ina rokon mutanen Adamawa suyi mana addu’a kuma Allah ya ban dukkan abin da zai bama dan adam a duniya shi kuma yasan abin dake jiranmu ranar kiyama.” Inji gwamnar.

“Allah shi ya sanya Alhaji Ummaru Jibrilla ya zama mahaifina, ya sanya na zama Musulmi, nayi Sanata na shekara hudu sannan nayi gwamna na shekara hudu sannan zan iya kasancewa a gwamna har shekara takwas. Babu wanda yasan gobe. Mulki nashi ne, kuma babu wanda yasan abin da ubangiji zayyi.

“Dan Adam bai san me Allah zai masa ba amman a yanzu a halin da nake ciki ina nagode ma Allah sosai kuma ina addu’ar zaman lafiya a Adamawa shi yasa muke nan har yanzu” Cewar Gwamna Bindow.