An hana yar gidan Sulaiman Adeleh shiga JAMB saboda taki cire hijab

1
197

Ma’aikacin jaridar nan Sulaiman Adeleh yace an hana ‘Yarshi shiga ajin zana jarabawar Jamb yau alhamis bayan da taqi cire hijabinta.

An hanata shiga Jamb din ne New Ocean School, Megida dake Ayobo kamar yacce ya bayyana a shafinsa na twitter.

Adeleh yace daga baya an barta ta shiga Jarabawar amman meye nasa musulmai suna cire hijab.

Kuma Hijabi bashi daya daga cikin abin da Hukumar Jarabawa ta jamb ta hana sakawa a wajen zana jarabawar.

Kamar yacce hukunar Jamb ta ruwaito mutane kusan Miliyan Biyu ne zasu zana jarabawar ta bana sannan akwai kayayyaki guda goma sha takwas da Hukumar ta hana amfani ko zuwa dasu lokacin Jarabawar amman ban da hijabi a ciki.