Daga Farfesa Ibrahim Malumfashi Zuwa Ga Shugaba Muhammadu Buhari (1)

0
71

A cikin tsawon shekara 35 ke nan nake tu’ammali da kai, wani lokacin a kaikaice, wato daga nesa kurum nake ganinka ko jin labarinka, musamman lokacin da ka dare Shugabancin kasar nan daga shekarar 1983, kana soja, cikin kakin da ba wanda ya isa ya tanka maka ko ya ce ka yi ba daidai ba, don kai ne da wuka da nama.

A lokacin ban kammala karatun jami’a ba, kuma lallai daga halin da kasar nan ta shiga a lokacin, na san mutane sun ji jiki, domin mu kan mu dalibai, mun ji jikin, ta fuskoki da dama da za mu iya karaswa. Abincin da ake ba mu kusan mu ce a kyauta a matsayin dalibai, wata sa’a har da rabin kaza kafin zuwan mulkinka, muka neme shi sama ko kasa, sai dai mu sanya kudi mu saya, kuma a lokacin an yi fatarar da kullum ke sa mu kokawa a zuci, wata sa’a kuma har a fili.

Amma daga baya mun ji dadin gwamnatinka, musamman daga shekarar 1984 lokacin da ka fara saita lamurra zuwa shekarar 1985 da muke yin hidimar kasa, za mu iya cewa kasar nan ta fara ganin hasken da zai kai ta ga tudun mun tsira, duk kuwa da cewa an sha wuya, ba ga ‘yan makaranta ba, har sauran al’ummar kasar baki daya, talakawa da masu tarin dukiya, balle kuma ‘yan siyasa da ka dinga daurewa, wasu har tsawon shekara 100!

Duk da cewa mulkinka a wancan lokaci ya dace da yanayin kasar, domin kuwa ta lalace ta kowace fuska, amma wahalar da aka sha da rayukan da aka rasa da talaucewar da aka yi ba abin da wasu za su manta da sauri ne ba. Ke nan zan iya cewa, bakin-farin-ciki ne ya kame al’ummarmu a lokacin.

Shi ya sa har abada ban mantawa da abin da ya faru a lokacin muna camp na hidimar kasa a birnin Yola, inda da asuba a wata rana a watan Agusta na 1985 da kwamnandan sojan da ke kula da mu ya taso mu cikin muku-mukun safiya ya ce da mu ‘yau ba fareti za mu yi ba, na tashe ku ne in gaya muku cewa an kawar da gwamnatin Janar Buhari, ban san dalilin yin haka ba, kuma bai dame ni ba, kowa ya koma xldaki.’

Ban taba mantawa da yanayin da muka samu kanmu a ciki, har da sojojin da ke kula da mu, daga masu tsaki, sai masu tofin Alla-tsine, irinmu da suke masoyanka tun a lokacin hawaye muka dinga zubarwa, domin mun yi amanna cewa abin da Janar Babangida ya yi maka, bai kyauta ba, ba kuma kai ne kadai bai kyauta wa ba, mu ne ya lalata wa tsari, kasar ce bai yi wa adalci ba, domin kuwa duk mai hankali yana da yakinin da ka dade a kan karagar mulki da kila kasar ta samu tudun dafawa, domin cigaba ta fuskoki da dama. Haka muka bar camp cikin alhini da damuwa, abubuwan da suka faru daga 1985 da Janar Babangida ya hau karagar mulki, har hawan Earnest Shonekan na rikon kwarya, abubuwa ne da ba sai na sake taliyon su a nan ba, ka san su, na san su, sauran al’umma da suka rayu daga wannan lokaci zuwa yau, sun san su, da alama kuma abin nan ne da za mu iya kira da shillon Biliya, wato mutum da ya faxldo daga saman itace ya zarce cikin rijiya.

Saboda haka ya Shugabana Muhammadu Buhari, ko da aka gayyaci ‘yan siyasa a 1998 zuwa 1999 don su shiga hada-hadar siyasa da zabe, kamar yadda mawakin nan Dan Shabiyu ya fada, domin a dana su, don an dauka adilai ne su, ashe ba a san azzalumai ne ba, ban yi mamakin da ka yi zamanka gida ka ki shiga cikin wannan hargidiballe ba, domin bisa ga dukkan alamu, siyasa ba kayanka ba ne, domin kai mutum ne mai kaifi daya, wanda ba zai iya rawa da ‘yan siyasa ba.

Na sauka hakan za ta kasance da rayuwarka har abada, wato ka yi ritaya daga rigingimun mulki da siyasa da neman gyara batattun lamurra. Sai dai kamar yadda na sani daga dan kusantarka da na soma yi daga baya, lokaci ne kawai bai yi ba, za ka koma ruwa, wato za a dama da kai kai tsaye a sha’anin mulki a kasar nan, musamman ganin shekarun da ka yi kana shugabancin hukumar PTF, karqashin mulkin Janar Abacha, inda ina jin cewa daga nan ne aka soma kara tabbatar da kai a matsayin mutum mai kamanta gaskiya, ko da kuwa wasu wadanda kake shugabancin tare da su, ba su da tabon gaskiyar tare da su.

Ya mai girma Shugaba Muhammadu Buhari, duk da cewa wasu daga cikin masoyanka tun kana shugaban kasa a tsakanin 1983 zuwa 1985, har zuwa lokacin da kake zaune a gida, da kuma lokacin da ka shugabanci PTF da kafa qungiyar The Buhari Organisation (TBO), wadda ina jin ita ce tushen shigarka tsundum cikin siyasa, ba duka suka amince da kundumawarka cikin harkokin mulki da siyasar ba, domin muna ganin za a bata maka suna ne, ko a yi amfani da kai domin a cimma wasu muradai na son rai na wasu mutane kalilan, amma wannan bai hana ka sunsunar siyasa da kuma jingina ga wasu madafun iko da mulki ba. Wannan zabinka ne, ba kuma wanda ya isa ya hana ka. Amma amsar da ka ba ni a lokacin da na taba tambayarka a gidanka, bayan ka dawo daga shugabancin PTF, bayan an rushe ta, ina jin ita ce dalilin kutsenka cikin siyasa da kuma dagewa da amincewa da batunci daga ‘yan siyasar da masoya.

Na san kai kila ka manta, amma ni har yau ban manta da tambayar da kuma amsar da ka ba ni ba, na dai ce da kai ‘shin ba ka jin ka yi nadamar karbar shugabancin PTF, ganin irin tonon sililin da ake ta yi na cewa ka yi wandaka ko kuma wasu na kusa da kai sun yi almuzarranci da dukiyar al’umma a matsayinka na Shugaban PTF?’

A lokacin nan na san tambayar ba ta yi ma dadi ba, musamman ganin cewa ina daga cikin wadanda ba su amince da ka amshi Shugabancin PTF ba, ina kuma gudun kada ‘yan Nijeriya su lalata man mai gaskiyar da nake so da kauna ne shi ya sa, ba wani dalili na daban ba!

Za Mu Ci Gaba