Mai kudin duniya zai saki matarsa tare da bata kudin da zata zama Mace ta uku a masu kudin duniya

0
124

Mai kamfanin Amazon kuma mutumin da yafi kowa kudi a duniya Jezz Bezos zai saki matarsa Mackenzie tare da bata Naira Triliyan Sha biyu da Rabi wanda hakan zai sa ta zama mace ta uku a kudi a duniya.

Mista Bezos yana da kudin da ya kai kwatankwacin Tiriliyan 53 kuma sunyi aure da Mackenzie a shekarar 1993 ne kuma suna da yara guda 4.

Duk da yake sakin zai mayar da Mackenzie a matsayin mace ta uku mafi kudi a duniya amman hakan bazai canza Mista Benzos a matsayin mutum na farko mafi kudi a duniya ba kamar yacce Jaridar Fobes ta ruwaito.

Yanzu dai Mackenzie zata amshi kaso 4 cikin dari na kamfanin Amazon wanda shine yayi daidai da Tiriliyan Sha biyi da Rabi.

Abin Mamaki Mackenzie kwanannan ta bude shafin twitter kuma maganarta na farko akan Rabuwarsu da Mijinta ne tayi. Ga dai twitter a kasa