Kotu ta Sallami mahaifiyar Maryam Sanda da ‘Yan uwanta

0
158

Babbar Kotu dake Maitama tayi watsi da zargin da ake ma Mahaifiyar Maryam Sanda da kuma yan uwanta bisa zargin suna da hannu wajen kisan Mijin Maryam Sanda wato Bilyaminu Bello wanda ita Maryam din ake zarginta da aikawa.

Mai shari’a Justice Yusuf Halilu ya sallami mahaifiyarta, Maimuna Aliyu; Dan uwanta, Aliyu Sanda da kuma ma’aikaciyarsu Sadiya Aminu, wanda ‘Yan Sanda suke zarginsu da laifin kisan.

Idan dai baza a manta ba tun Shekarar data wuce ne ake zargin Maryam Sanda da kashe mijinta ta hanyar amfani da wuqa ta daba masa a wuyarshi . Kotun ta daga sauraron karar zuwa 6 ga watan Mayun wannan shekarar.