Shin da gaske ne Buhari bai damu da Rayuwar Yan arewa ba?

0
48

Daga Rahma Abdulmajid

ME MUKE JIRA BAYAN WANNAN?
Duk wata shaida ta cewa Buhari bai damu da rayukanmu a Arewa ba ta samu…

A wannan satin ne Arewa kekoka wa daruruwan rayuka da suka salwanta tsakanin Kisan kiyashi a Zamfara da sace-sacen al’umma akan hanyoyin barin gari, Amma babu jaje daga shugaban kasa sai ma hango shi da ake yana shewa a Senegal.

A satin da ya gabata ne aka sako malamin addininnan dakyar daga hannun masu satar mutane bayan da aka sace shi biyo bayan cusa nemar wa Buhari 4+4 DA yayi a adduarsa ta khatma, nan ma babu jaje daga shugaban kasa hana rantsuwa malamin ya je ya durkusa ya gaida Ganduje

A sati na can sama Jihar Kano kuma shalkwatar filin soyayyar Buhari tayi fama da kutsen ‘yandaba a harkar siyasa wanda duniya ta nuna. A nan ma sai bayan sati2 ne aka ji Garba Shehu na cewa me ake so shugaban kasar yayi?

Amma Ranar Lahadin nan yansandan SARS sun kashe wani bayerabe garin zarginsa da laifi, washe gari litinin an jiwo babatun shugaban kasar ta Oduduwa yana lasar takobin ba zai yarda ba sai an bi masa kadin dan uwa bayeraba Kolade. Har ma ya tura yansanda durkushe gwiwa bibbiyu suna baiwa iyalan mamacin hakuri duk da tuni suka kama ‘yan uwansu ‘yansanda da ake zargi da lamarin. Ga dai hotunan kalaman shugaban a Twitter da kuma yansanda masu ban hakuri