Wai Shin Zamfarawa Ba Bil’adama Bane

0
46

Daga Kais Daud Sallau

Na dade ina tunani, ina nazari game da abubuwan da suke faruwa a jihar Zamfara. A duk lokacin da naga rahoto daga jihar Zamfara sai gaba na ya tashi, domin kawai abinda nake fara tunawa shine an tayarwa ‘yan’uwan mu da hankali. Domin daga kaji an sace wani, sai kaji ‘yan bindiga sun kai hari wani gari sun kashe mutane.

Hankalina na matukar tashi game da labarin Zamfara, har kasa bacci nake yi saboda’ yan’uwan mu na cikin tashin hankali, nace ko minista tsaro Gen. Mansur Dan-ali ba daga Zamfara ya ke ba ne, sai in sake ce ko shugaban kasa Muhammadu Buhari baya samun labarin halin da ‘yan jihar Zamfara suke ciki.

A duk ranan Allah sai an sace ko an kashe mutane a jihar Zamfara, gwamnatin tarayya da jami’an tsaro duk sun mai da hankali su fada da Boko Haram, su kuma’ yan ta’adda suna amfani da wannan dama sai barna suke yi a wadansu jihohi.

JAN HANKALI

Ina jan hankali shugaban kasa Muhammadu Buhari, jami’an tsaro da su mayar da hankalin jihar Zamfara, domin mutanen jihar Zamfara suna cikin kunci, a kullum rayuwar su na cikin baraza na, suna bukatan dauki daga gwamnatin tarayya cikin gaggawa.

Allah ya ba da zaman lafiya a jihar Zamfara, dama kasar mu Nijeriya. Amen.