An kai harin da ya hallaka mutum kusan 50 a wasu kauyukan Zamfara

0
48

Wasu da ake zargi ‘yan bindiga dadi ne sun kai hari a wasu kauyuka da ke karamar hukumar Shinkafi dake Jihar Zamfara inda mazauna yankin suka ce ”an kashe a kalla mutum 42.”
Maharan dai sun kai harin ne a kauyukan da suka hada da Kurya da Kursasa da wasu kauyuka da ke yankin inda suka yi ta harbin mai uwa da wabi.
A kwanakin baya ne dai gwamnan jihar Abdullaziz Yari ya bayyana cewa maharan da ke kai hari na amfani ne da bindigogi “na al’ada” wato kanannan bindigogi inda kuma jami’an tsaro na amfani da manyan bindigogi inda ya bukaci jami’an tasron da su fito su yi amfani da manyan bindigoginsu domin yakar maharan.