El-Rufa’i zai sauka daga Kujerar Gwamna

3
1250

Gwamnar Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i zai sauka daga kan kujerarsa ta Gwamna idan buhari ya amince zai bashi wani mukami mai girma a fadar shugaban kasa kamar yacce Jaridar The will Nigeria ta wannan satin ta rubuta.

A cewar Jaridar labarurruka da yawa sunzo mata akan wannan zancen infa El-Rufa’i yake neman masu bama shugaban kasa shawara su amince a bashi mukamin “Chief of Staff” ko kuma “Principal Secretary to the president”.

Majiyar ta shaidama jaridar cewa El-Rufa’i ya ta zabi mataimakiyar sa musulma ne (Muslim/Muslim ticket) a zaben gwamnan daya wuce saboda yana son ya koma fadar shugaban kasa.

A cewarsa wani da yace kada a ambaci sunansa yace, gwamnar ya fada cewa “Idan Shugaban Kasa ya zabeni zan sauka daga mukamin Gwamnar Jihar Kaduna sannan mataimakiyata Hadiza zata zama gwamna, sai ta zabi kirista ya zama matamakinta daman ni burina shine gwamna ya kasance musulmi”

El-Rufa’i ya gana da shugaban Kasa har sau hudu a satin nan daya gabata a sirrance saboda wannan burin nasa.

El-Rufa’i shine wanda ya kayar da babban abokin hamayyarsa ta jam’iyyar PDP Isa Ashiru Kudan a zaben daya gabata.

3 COMMENTS

  1. Gaskiya ban Gamsu da wannan tunanin na gwamna El rufai ba saboda ahalin Yanzu irin shi ne kawai ya kamata jihar Kaduna ta samu amatsayin gwamna laakari da yanda aka samu qaranxin rikicin addini da na qabilanci a jahar a tenuwar nan da zata qare