Zababben gwamnar Adamawa yayi alkawarin biyan Mafi karancin albashi 30,000

0
26

Zababben Gwamnar Jihar Adamawa Fintir yayi alkawarin Biyan albashi mafi karanci na naira dubu talatin ga ma’aikatar Jihar Adamawa.

Fintiri yayi nasarar zaben ne a karkashin Jam’iyyar PDP bayan daya doke jam’iyya maici APC a makondaya gabata.

Acewarsq: “Zan ba ma’aikatar gwamnati kulawa na mussamman sannan zan kara inganta ta.

“Domin tabbatar da muhimmancin haka, ni zan fara aiwatar da shi, domin kada mu fuskanci yajin aikin ma’aikata,” inji Fintiri.

Ya kara da cewa “Mutane sun bamu kuri’unsu kuma Allah ya tabbatar da hakan a yau. Za mu tabbatar ganin cewa mun isar da alkawaran zaben da muka dauka”.