Shugaba Buhari ya daina Sallar Jumma’ah a babban Masallaci na Abuja

0
80

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yanke shawarar daina a Babban Masallaci na Abuja inda yace zai dinga yin Sallar Jumma’ar ne a masallacin fadar shugaban Kasa.

Yace ya yanke shawarar ne bayan nazari da yayi da kuma lura da mutane yacce suke shan wahala duk lokacin da zai yi sallar Jumma’ah a babban masallacin saboda cinkosa da fitarsa ke janyowa al’umma.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya ce shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke amsa tambaya da tawagar limamai da manyan malaman addinin musulunci daga jihohi Najeriya suka yi masa yayin da suka kai masa ziyara a ranar Juma’a.

Shugaban kasar ya ce: “A kan batun bukatar da kuka gabatar na nema in rinka zuwa sallar Juma’a a masallacin kasa, Ina rokon ku da ku fahimta cewa na fara yin sallar Juma’a ne a masallacin fadar shugaban kasa saboda in rage wahalhalun al’umma ke shiga idan na fita.

“Kamar yadda kuka sani, duk lokacin da shugaban kasa zai fita dole sai an takaita zirga-zirga a wasu wurare tare da kafa shinge a hanyoyi wanda hakan na iya janyo matsi ga masallata da sauran al’umma.”