Mutane miliyan 26 ne suka nemi aikin NNPC

0
33

A wani rohoto da Jaridar Sun ta fitar tace Mutane Miliyan 26 ne suka nemi aikin Hukumar NNPC wadanda suka hada da masu HND, Degree da masu masters.

An rufe shafin daura takardun karatun a ranar Talata, 26 ga watan Maris, 2019.

Wata majiya mai karfi ta bayyanawa Daily Sun cewa yawan mutane milyan 25.6 da suka nemi aikin ya razana shugabannin NNPC da kuma gwamnatin tarayya saboda hakan na nuna cewa akwai babban kalubalen rashin aikin yi a Najeriya.

Rahoton NBS ya nuna cewa yawan mutanen da basu aikin komai ku kuma basu wani aikin kirki ya tashi daga milyan 17.6 a karshen shekarar 2017 zuwa 20.9 a shekarar 2018.

Idan ba’a manta ba hukumar NNPC ta dade bata dauki ma’aikata ba sannan kuma Nigeria tana daya daga cikin Kasashen African da take da yawan yan Boko wadanda basu da aikinyi.