Ya saci burodin 300 sannan kotu taci tararsa 150,000

0
43

A jiya be kotu a Jihar Lagos ta yanke ma wani mutun mai suna Lukman Babatunde tarar Naira dubu Dari da Hansin bayan kamashi da tayi da laifin satar Burodi da sabulu na Naira dari Uku a wani shago.

Babatunde mazaunin Lagos mai shekara 62 kotu ta tuhumeshu da laifin kuma bayyi musun hakan ba.
Mai kawo karar, Sergeant Modupe Olaluwoye, ta bayyanawa kotu cewa mai laifin ya aikata laifin ranar 16 ga watan Mayu da misalin karfe 4 na yamman ranar ne, a wani babban shago mai suna Trolleys, dake unguwar Yaba, cikin jihar ta Lagos.