Atiku yayi alkawarin biyan kudin da za’a fanso Malam Ahmad Sulaiman

0
70

Tsohon mataimakin Shugaban Kasar Nijeriya kuma wanda ya fadi zabe a zaben shugabancin kasar daya gudana watan daya gabata yayi alkawarin biyan kudin fansa har Naira Miliyan 300 don a ceto ran Malam Ahmad Sulaiman.

Idan baza’a manta ba Malam Ahmad Sulaiman masu kamen mutane ne suka kamashi kusan sati biyu da suka gabata inda kuma suka nemi sai an biyasu kudi har naira miliyan 300 kafin a sakoshi .

A wanu faifen bayanai da akaji daga bakin Malam Ahmad din ya bukaci yan uwanshi su siyar da motarsa da gudajensa don a samu a hada kudin amman dai yanzu Atiku yace zai biya