Masu garkuwa da Alaramma Malam Ahmad Sulaiman sun bukaci a basu Naira Miliyan 300

0
39

Idan ba’a manta ba yau kusan sati daya da yin garkuwa da Alaramma Malam Ahmad sulaiman tare da wasu abokanansa. Yanzu masu harkuwar sun nemi sai an basu naira miliyan dari uku kafin su sauko da alarammar. Duk da yake yan uwansa sun koka kan rashin lafiyar da yake fama da ita kuma masu garkuwar haka suma daukeshu ba tare da tafiya da maganin da likita yace ya dinga sha ba.

A yanzu haka yan uwa musulmai sun dukufa da yin addu’o’i akan Allah ya tsare alarammar ya kuma sa a sakoshi cikin koshin lafia