Yacce Okorocha ya wuwure Naira Biliyan 17 a cikin kwana biyu kacal

0
37

Jam’iyyar PDP ta koka kan yacce Okocha ya wuwure Naira Biliyan 17 daga aljihun gwamnatin jihar Imo a kwanaki biyu kacal

cewar wata sanarwa dauke da sa hannun babban lauya Charles Ezekwm, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Imo, “daga ranar 12 ga watan Maris da ranar Alhamis 14 ga watan Maris 2019, gwamna Rochas Okorocha ya cire kudade daga bankunan Access, Zenith, Unity da kuma bankin Skye wanda suka haura 17bn.

Jam’iyyar da kara da cewar ya kuma dauki wasu kayayyaki daga gidan gwamnatin jihar wanda ya hada har da kayan wuta yasa aka mai dasu gidansa