INEC ta hana Atiku duba kayayyakin zabe

0
18

Babban jam’iyyar adawa ta Nijeriya PDP ta koka da cewar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta h

ana atiku duba kayayyakin zabe.

Jam’iyyar PDP ta saki wannna jawabin be da sanyin safiyar nan inda tace:

” Yana da muhimmanci mu sanar da yan Najeriya cewa bayan samun hukuncin kotu, wanda ke baiwa INEC umurnin baiwa Atiku da PDP takardun da akayi amfani da su wajen zaben shugaban kasa.”
“Lauyoyinmu sun rubutawa shugaban INEC wasika a ranar 11 da 12 ga watan Maris 2019. Duk da wasikar kotu da wasiku daban-daban da muka turawa INEC, hukumar ta hana PDP da Atiku Abubakar ganin takardu da kayayyakin aikin zabe.”
“Shugabancin INEC da APC na kokarin kawo mana cikas a kotu, saboda su gano cewa takardun zaben zai nuna cewa Atiku Abubakar ne ya lashe zaben da jama’a suka kada a rumfunan zabensu.”