Hukumar INEC ta fitar da sabbin bayanai akan zaben gwamnan Adamawa

0
42

Hukumar ta kasa wato INEC ta bayyana cewa za’a sake gudanar da zabukan ne a kananan hukumomi 14, mazabu 29 kuma rumfunan zabe 44 da ke da mutanen da suka yi rijista sama da dubu arba’in.

Babban kwamishin hukumar ta INEC a jihar Adamawa, Kasim Gaidam ne ya bayyanawa manema labarai yau din nan aofishin sa dake a garin Yola, babban birnin jihar ta Adamawa.
A cewar sa, hukumar kawo yanzu ta kammala dukkan shirye-shiryen ta don gudanar da zaben tare kuma da bayar da tabbacin yi wa kowa adalci a yayin zaben.
Yace, kananan hukumomin da za’a sake zaben a jihar sun hada da Yola ta kudu, Fufore, Ganye, Girei, Guyuk da kuma Hong, Lamurde, Numan, Madagali, Michika, Mubi North, Shelleng, Song da kuma karamar hukumar Toungo.