Shugaba izala ya fadi gaskiya akan wasikar yarjejeniyarsu da gwamna El-Rufa’i

0
33

Shugaban kungiyar jama’atu izalatul bid’a wa ika matus sunna (JIBWIS) reshen jihar Kaduna, Imam Tukur Isa, ya nesanta kungiyar su daga wata takardar kulla yarjejeniyar hana shugaban darikar Tijjaniya, Dahiru Bauchi, gudanar da taron mauludi a Kaduna.

Imam Tukur ya yi wadannan kalamai ne yayin gabatar da jawabi ga manema labarai bayan kamala wani taro da kungiyar ‘Yan uwa Musulman Kaduna da aka yi a cikin garin Kaduna.