Kotu ta amince Abba Yusuf (Abba Gida Gida) yayi takara

0
61

Wata Kotun daukaka kara dake jihar Kaduna ta yi watsi da hukuncin da wata kotun tarayya ta jihar Kano ta zartar wacce ta rushe zaben da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar Kano wanda ya bai wa Abba Kabir Yusuf damar zama dan takarar gwamna a jam’iyyar.

Idan baza a iya mantawa ba a ranar litinin da ta gabata ne kotun tarayya dake kano ta dakatar da Abba daga shiga takaran gwamnar kano. Inda tace an zabeshi ne ba bisa adalci ba.