Ku zabi ra’ayinku a zaben gwamnoni kada kuyi sak ____Buhari

0
31
buhari
NIGERIA PMB

Shugaban Kasar Nigeria yayi kira ga yan Nigeria da su zabi cancanta a zaben gwamnoni dana yan majalisu da za’ayi sati mai zuwa.

Shugaba Buhari yayi kiran ne a yaron da yayi da manema labarai inda yace “koda mutun yana jam’iyyarmu ko kuma bashi a cikinta idan yafi wanda yake APC cancanta to ku zabeshi”

Sannna yayi kira ga yan Nigeria da su tabbatar sunyi zabe ba tare da tashin hankali ba. Ya kuma sake tabbatar ma da yan Nijeriya cewa zai yi iya ka kokarinsa ganin anyi zabe ba tare da wani magudi ba.

A cewarshi “Ina kira da shugana zabe da kada ya bayar da wata kofa ta magudin zabe sannan muma zanu tabbatar da anyi zabe cikin gaskiya da adalci”.

Idan ba’a manta ba sati biyu da suka wuce ne akayi zaben shugaban kasa inda ya kayar da abokin hamayyarshi na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar. Sakamakon da shi Atikun yace bai amince dashi ba