Dalilin dakatar da Abba Gida Gida daga takarar gwamna

0
78

Babbar kotun dake jihar kani tun a safiyar litinin din daya ganata ne ta dakatar da Abba K Yusuf daga takarar gwamnar kano abin da wasu masoyansa suka qalubalanta. Kotun ta tarayya a Kano ta yanke hukuncin cewa zaben fitar da ‘yan takara da aka tsayar da Abba haramtacce ne.

A ewar Kotun, ta ce ba a yi zaben fitar da dan takarar gwamna ba a Kano tare da umurtar a sake wani sabon zabe tsakanin litinin zuwa juma’a.
Wanda ya shigar da karar yana kalubalantar jam’iyyar PDP ne da hukumar zabe.

Kotun ta amince ne da karar da bangaren Ali Amin-little ya shigar wadanda suka bukaci kotu ta tabbatar da cewa PDP ba ta yi zaben fitar da gwani ba a Kano.
Kukuncin kotun na nufin zaben da jam’iyyar PDP ta gudanar a jihar Kano wanda ya bai wa Abba Kabir Yusuf takara ba daidai ba ne.