Atiku ne yaci zaben 2019 – Buba Galadima

0
27

Buba Galadima ya ce jam’iyyarsu ta PDP ta ba Atiku Abubakar cikakken goyon bayan don ya kalubalanci zaben 2019 a gaban kotu.
Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP sun yi watsi da sakamakon zaben 2019 da ka gudanar a makon daya gabata bisa zargin an tafka magudi a zaben, kuma Atikun ya ce zai garzaya kotu.
Sai dai jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta musanta cewa an tafka magudi a zaben.
Buba Galadima Yace suna da hujjoji da za su gabatar a gaban kotu da ke nuna cewa “mu ne muka ci zabe. Don haka, dole a bai wa dan takarar shugabancin Najeriya,”
Galadima yayi zargin cewa dan takararsu yana fuskantar matsin lambar kan kada ya kai batun gaban kotu.
Ya ce hakan na faruwa ne saboda jam’iyyar APC tana tsoron hujjojin da za su gabatar a gaban kotu.