Zabe 2019: anyi wa ma’aikatan zabe fyade an kuma sace wasu

0
31

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta ce an sace wasu daga cikin ma’aikatan ta na wucin gadi tare da yi wa wasu matan fyade yayin gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da aka yi a ranar asabar din daya gabata.

kwamishin yada labarai da wayar da kan ma su zabe, Festus Okoye ya bayyana cewa “Bayan cin zarafin ma’ikatan mu tare yi masu baraxana, an sace wasu, an yi wa wasu fyade,”
Ya kara da cewa
Mu na yi wa ‘yan uwa da dangin ma’aikatan mu na wucin gadi ta’aziyyar ‘yan uwan su da su ka rasa ran su yayin gudanar da aikin su .”
“ INEC ta kamala shiri domin ganin ba a sake samun afkuwar irin matsalolin da aka fuskanta a zaben da za ta gudanar na gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi ranar 9 ga watan Maris .”