Da gaske Dasuki ya rasu?

0
67

Tun farkon wannan shekarar ne ake ta yada rade radin cewa tsohon mai bama shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro Sambo dasuki ya rasu amman hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta karyata labarin da ake ta yadawa.

Kakakin hukumar Peter Afunanya ya shaida wa kafar talabijin ta kasa NTA cewa labarin karya ne ake yada wa, yana mai cewa “ba wai yana raye ba ne kawai, yana kuma cikin koshin lafiya.”

Ana dai ci gaba da tsare Dasuki ne duk da umarnin kotun Tarayya ta bayar na ayi beli, har da kotun ECOWAS itama ta bayar da umarnin bayar belinsa amman gwamnatin tarayya tari musisi da lamarin.