Zabe 2019: Wasu yan bindiga sun sace ma’aikacin zabe sun kuma ‘kona wajen

0
45
election-violence

election-violence

 

Wasu yan bindiga da ba’a san ko su waye ba sun sace baturen zabe sannan suka kona wajen.a

Yn bindigan sun yi awon gaba da babban jami’in zabe na karamar hukumar Orlu ta Jihar Imo, Mista December Aloy Njoku tare baturen zabe dake tattara sakamakon zaben Sanata na mazabar Orlu, zaben da aka ruwaito Rochas ya lashe.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 14 ga watan Feburairu, inda a ranar kuma aka samu wasu bata gari suka banka ma ofishin INEC dake karamar hukumar Isiala Mbano na jahar ta Imo, sai dai ba haka banza lamarin ya auku ba.

nigeria election

Majiyarmu ta arewadesire ta tabbata da cewa an samu wannan matsala ne jim kada bayan jami’an biyu sun dakatar da sanar da sakamakon zaben daya gudana a kananan hukumomin jahar guda goma sha daya cikin goma sha biyu dake mazabar, bayan sun fahimci akwai yan matsaloli tattare da sakamakon.
Gwamnan jahar, Okorocha shine dan takarar Sanatan APC na mazabar, yayin da Jones Onyereri ke takara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, sai dai a sanadiyyar wannan tsaiko da aka samu ta sa kwamishinan INEC na jahar ya bada umarnin dakatar da sanarwar.