Zabe 2019: Buhari ya lashe zabe a karamar hukumar Atiku dake adamawa

0
57
buhari
NIGERIA PMB

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP mai hammaya wato Alhaji Atiku Abubakar yasha kaye a karamar hukumarsa da ke jihar Adamawa a hannun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ne ya samu rinjayen kuri’u a karamar hukumar Yola ta arewa.

Atiku  Abubakar ya samu kuri’u 27,789, yayin da kuma abokin hamayyarsa Buhari ya samu kuri’u 43,865, kamar yadda Dr. Oye babban jami’in da ke tattara sakamakon zaben shugaban kasar na karamar hukumar ya tabbatar.
Atiku ya sha kaye tun a rumfar unguwarsa da ya kada kuri’a tare da iyalinsa.
Shugaba Buhari ne ya lashe zaben a rumfar ta babban abokin hammayarsa na PDP Atiku Abubakar.
Jam’iyyar APC ta samu kuri’a 186, yayin da PDP ta samu 167.